Shirin Radio D zango na 1 | Koyon Jamusanci | Deutsche Welle

Shirin Radio D zango na 1 | Koyon Jamusanci |...

Release Date

All Episodes

Kashi na 26 – Ban-kwana da Ayhan

Wannan rana ce ta bakin ciki a ofishin Radio D. Domin kuwa Ayhan yana ban-kwana kuma zai koma kasar Turkiyya. Duk da cewa abokan aikinsa sun shirya masa walima ta ba-zata, wannan bai kwantar masa da hankali ba. Paula ta zo aiki da safe ta samu kowa yana shirye-shiryen zuwa walima ...  Show more

Kashi na 25 – Tarbar jiragen ruwa

'Yan jaridar sun yi kokarin gano ma'anar kalmar "getürkt", don haka suka kai ziyara wata gabar teku, inda kowane jirgi da irin tarbar da ake yi masa.A gabar tekun Willkomm-Höft, ana tarbar kowane jirgi ne da taken kasar da yake dauke da tutarta. A wasansu na rediyo, Paula da Phil ...  Show more

Kashi na 24 – Daga teburin edita

Mujiya Eulalia ta taimaka wajen sa Paula da Philipp kan hanya. Sun gano cewa ashe abokan aikinsu da ke aiki a jaridar Hamburg na da hannu a cikin wannan al'amari. Paula da Philipp da mujiya Eulalia sun gano cewa ashe jaridar Hamburg ce ta shirya wannan abu a gabar teku domin su y ...  Show more

Kashi na 23 – Kayar kifin "shark"

Paula da Philipp sun warware matsalar ganin kifin "shark", sannan kuma sun sake gano wata damfara. Amma, har yanzu ba a gano dalilin da ya kawo wannan ba. Yayin da ake neman mai wasan sululun kan ruwa, Paula da Philipp kuma sun hadu da wani mai iyo, sun kuma gano bakin zaren. Mai ...  Show more

Kashi na 22 – Batcaccen dan sululun ruwa

Philipp da Paula sun bi sawun kifin "shark" inda suka gano abubuwan ban-mamaki. Ga allon wasa amma kuma ba mahayinsa a gabar tekun, kuma wani labari a cikin wata jarida ya dauki hankalinsu. Da suka bar wajen hayaniyar da ake ciki, sai 'yan jaridar suka shiga binciken ko za su ga ...  Show more